An kama tsoffin ma’aikatan banki bisa zargin satar kuɗi daga asusun kwastoman da ya mutu
Daga Sabiu Abdullahi
Jami’an hukumar shiyyar Makurdi na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) sun kama wasu tsofaffin ma’aikatan bankin Union guda biyu, Idah Ogoh da Agbo Okwute bisa zargin yin sama da fadi da N4,199,500 na asusun ajiyar wani kwastoman da ya rasu.
An kama mutanen ne a ranar 21 ga watan Yuni, 2024, biyo bayan korafin da bankin ya yi kan cirar kudi ba tare da izini ba a asusun Emmanuel Azer Agenna, wanda shi ne kwastoman da ya mutu ɗin.
A binciken da bankin ya gudanar, Ogoh, wanda tsohon ma’aikaci ne, ya sayi katin cire kudi na asusun marigayin, inda daga bisani ya mika shi ga Okwute.
An dai yi zargin cewa su biyun sun yi amfani da katin ne wajen fitar da kudade daga asusun ta hannun wani daban.
Hukumar EFCC za ta gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.