January 14, 2025

An kama mutum 8 da ake zargi sun kashe malamin Jami’ar Maiduguri

5
images-1-26.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Ƴan sanda a jihar Borno sun kama mutum takwas da ake zargin suna da hannu a kisan wani malami da ke koyarwa a sashen ilimin motsa jiki da ke Jami’ar Maiduguri, a jihar Borno.

Kakakin rundunar ASP Daso Kenneth, ya faɗa wa manema labarai cewa waɗanda ake zargin an kama su ne bayan wani rahoto da babban jami’in tsaron jami’ar ya shigar.

Ya ƙara da cewa babban jami’in da ke gadin jami’ar ya kai rahoto ofishin ƴan sanda da safe cewa an ga wata gawa a ofishi wadda aka gano ta Dakta Abdulkadir Kamal ce.

Kakakin ya ƙara da cewa da samun rahoton, aka aike ƴan sanda zuwa wajen inda kuma aka kai gawar asibiti domin yin bincike a kanta.

Ya faɗa cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano mutanen da ke da hannu a aika-aikar duk da cewa sun kama mutum takwas da ake zargi suna da hannu a kisan malamin.

5 thoughts on “An kama mutum 8 da ake zargi sun kashe malamin Jami’ar Maiduguri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *