An kama mahajjatan bogi ƴan Najeriya a Saudiyya
Daga Sabiu Abdullahi
A ranar Juma’a ne jami’an hukumar NAHCON suka kama wasu ‘yan Najeriya biyu da suka bayyana a matsayin mahajjata bogi a sansanin Muna da ke kasar Saudiyya.
An kama mahajjatan, Abu Mahmud da Ismaila Yahaya, suna cudanya da mahajjata na gaskiya wadanda ke hutawa bayan tafiyarsu daga Makka zuwa sansanin na Muna.
An gano mahajjatan jabun sanye da jabun katin shaida na Nusuk tare da sanya fararen ƙyallaye da alhazan ke sanyawa a kokarinsu shiga da jama’a.
Sai dai Mahmud wanda ya yi ikirarin cewa shi dan asalin jihar Kano ne, shi ma an same shi da takardar izinin shiga kasar Saudiyya da ta yi isfaya.
Ya kuma bayyana cewa yana zaune a Saudiyya tun a shekarar 2022 da biza wacce ta riga ta yi isfaya.
A kokarinsa na neman rayuwa mai kyau, an yi zargin cewa ya biya Naira miliyan 3 don shiga kasar Saudiyya don neman ‘nagartacciyar rayuwa ba bisa ka’ida ba.
“Aikin Hajji kawai nake so. Don haka sai na yi jabun Nusuk ID na kutsa kai cikin sansanin a lokacin da ’yan Najeriya suka iso da yammacin yau.
“Na yi hakuri. Don Allah a bar ni in tafi. Ba zan kara yin Hajji ba. Idan ka kama ni zan shiga cikin matsala da kuma dangina,” a cewarsa.
A halin yanzu dai jami’an hukumar NAHCON na ci gaba da yi wa mahajjatan tambayoyi, inda daga bisani za su mika su ga hukumomin Saudiyya.
rüyada su bardağı görmek