December 7, 2025

An hana wuraren ibada a Enugu saka lasifika a bainar jama’a

images (8) (1)

Daga Sodiqat Aisha Umar

Gwamnatin jihar Enugu ta ba da oda ga dukkanin majami’u da masallatai a jihar da su cire duk wata lasifika da suka sa a wajen gine-ginensu cikin kwana 90.

Gwamnatin ta kuma ce su dauki matakan tabbatar da cewa hayaniya ko karar abubuwan da ake yi a cikin wuraren ibadar ba ta fitowa bainar jama’a.

An dauki matakin ne a jiya Alhamis, a lokacin wani taro tsakanin hukumomin da shugabannin Kiristoci da Musulmi a jihar, kan aiwatar da tsarin gwamnatin jihar na takaita hayaniya.

Manema labarai su rawaito cewa shugaban hukumar raya babban birnin jihar ta Enugu, Uche Anya, wanda ya bayar da umarnin ya ce hayaniya da kara sun zama babbar matsala ga jihar.

Shugaban ya nuna takaicin yadda ofishinsa ya samu koke sama da 1,000, daga masu gidaje a kusa da wasu coci-coci da masallatai da wuraren rawa ko shaye-shaye da makamantansu a kan kara ko hayaniya da ke damunsu

A shekarar da ta wuce, 2023, gwamnatin jihar, da ke kudu maso gabas, a wani mataki na sake tsarin raya biranenta, ta umarci dukkanin wuraren nishadi da sharholiya da shaye-shaye da kade-kade da sauran abubuwa na walwala da su takaita hayaniyar da ake yi a wuraren, a babban birnin jihar, musamman ma a unguwannin da gidajen jama’a suke.

1 thought on “An hana wuraren ibada a Enugu saka lasifika a bainar jama’a

  1. Арматура диаметром 32 мм, изготовленная из стали марки А500С, является одним из самых востребованных видов металлопроката в строительстве. Она применяется при возведении фундаментов, армировании стен и перемычек. https://armatura32.ru

Comments are closed.