‘An gano harsasai 38 cikin kaina,’ Inji Zakzaky bayan dawowarsa daga Jinya a Iran
Daga Sabiu Abdullahi
Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Ibrahim El-zakzaky, a wani faifan bidiy, ya bayyana cewa an gano harsashi 38 a cikin kansa a lokacin da yake jinya a kasar Iran, sakamakon hatsaniya da suka yi da sojojin Najeriya a watan Disambar 2015 a Zariya.
Wannan dai na zuwa ne bayan wata doguwar jinya da ya shafe watanni biyar yana yi a kasar Iran.
Dawowarsa tare da matarsa ya haifar da murna yayin da dubban magoya bayansu suka tarbe su a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe kafin su wuce filin wasa na Moshood Abiola domin yin gagarumin taro.
A cikin faifan bidiyon, an ji Zakzaky yana cewa, “Duk Likitocin da suka duba sun ce wannan al’amari ne na Ubangiji. Akwai wani likitan ido, Dokta Shuaib, wanda ya ce a gaskiya abu ne ba mai yiwuwa ba a ce wani karfe ya huda ido kuma a ce idon yana aiki. Wasu karafa ne suka huda idona yayin da aka cire su aka yi wa ido magani. Wannan daga Allah ne.
An kuma jiyo shi yana cewa harsashi 38 likitoci suka samu a cikin idonsa.
Kalamansa sun haifar da cece-kuce sosai, domin da yawa sun dauki ikirarin nasa ba gaskiya ba ne kuma da wuya a iya yadda da shi.




