An Ga Watan Shawwal a Saudiyya
A yau Asabar, 29 ga Maris, 2025, ne hukumomin Saudiya suka tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal 1446 a kasar, wanda hakan ke nufin cewa gobe Lahadi, 30 ga Maris, 2025, ita ce ranar Idi.
Ganin watan Shawwal na nufin cewa an kammala azumin watan Ramadan na bana, kuma al’ummar Musulmi a fadin duniya za su gudanar da bukukuwan Eid El-Fitr.
Hukumomin addini a Saudiyya sun sanar da cewa an ga jinjirin wata a wurare daban-daban na kasar, wanda ya tabbatar da cewa watan Ramadan ya kare da kwanaki 29.
Saboda haka, Musulmi za su fara sabon wata na Shawwal gobe Lahadi.
Ana sa ran miliyoyin Musulmi za su hallara a masallatai da filayen idi domin gudanar da sallar Eid El-Fitr tare da yin addu’o’in samun zaman lafiya da albarka a duniya baki daya.


