An fara kama ƴan Najeriya a Libya bayan hukuncin da CAF ta yanke
Daga Sabiu Abdullahi
Bayan hukuncin da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta yanke dangane da korafin da Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta gabatar kan cin zarafin da aka yi wa tawagar Super Eagles a kasar Libiya, wasu daga ƴan Najeriya sun ruwaito cewa an kama mutane ƴan ƙasar da dama tare da ci musu tara a kasar.
Idan ba a manta ba, an tsare tawagar kwallon kafa ta Najeriya a filin jirgin sama na Al-Abraq da ke gabashin Libiya na tsawon sa’o’i fiye da 20 bayan isowarsu domin buga wasan zagaye na biyu na neman cancantar shiga gasar cin Kofin Afirka ta 2025 tsakaninsu da tawagar Libiya.
An tsara tawagar za su sauka a filin jirgin sama na Benghazi sannan su yi tafiyar kusan sa’o’i hudu a mota zuwa Benina, inda za a gudanar da wasan.
Sai dai kafin su sauka awa daya, matukin jirgin daga kasar Tunisiya ya samu umarni daga mahukuntan Libiya da su karkatar da jirgin zuwa filin jirgin sama na Al-Abraq, wanda ke nisan mil 150 daga inda za a buga wasan.
Wannan lamari ya haifar da fushi sosai, wanda ya sa NFF ta janye Super Eagles daga wasan neman cancantar sannan ta shigar da korafi a hukumance ga CAF.
A cikin hukuncin da ta yanke ranar Asabar, 26 ga Oktoba, wanda Shugaban Hukumar Ladabtarwa na CAF, Ousmane Kane, ya sanya wa hannu, hukumar ta ba Super Eagles na Najeriya maki uku da kwallaye uku kan wasan da aka dakatar.
Hukumar ladabtarwar ta bayyana cewa Hukumar Kwallon Kafa ta Libiya ta karya Sashe na 31 na Dokokin Gasar Cin Kofin Afirka da kuma sassa na 82 da 151 na Kundin Ladabtarwa na CAF.
Wani dan Najeriya mai zama a Tripoli, babban birnin kasar Libiya, Adenaike Emmanuel, ya ce an fara kama mutane tun ranar Lahadi bayan sanarwar CAF ta fito a kasar.
“Sun riga sun fara. Labarin ya fito ranar Asabar, kuma suna cewa ba za su yarda ba, ba su ne za su biya kudin ba. Sun fara nuna hakan.
“Wani ya kira ni ya ce an fara kama mutane a yankin da yake. Haka ma ake yi a nan Tripoli. A wasu wurare, an kama mutane da safiya da rana ranar Lahadi. Kamar yadda na fada a baya, ‘yan Libiya ba sa boye abin da suke ji. Sun yi imani cewa yin hakan zai ba su damar daukar fansa,” inji Adenaike.