An dawo da gawar tsohon gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu Najeriya

Daga Sabiu Abdullahi
Gawar tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ta iso Najeriya.
An shigo da gawar Akeredolu kasar ne daga Jamus, inda ya rasu kuma an ce an ajiye shi a dakin ajiye gawa har zuwa lokacin da za a binne shi.
Tsohon gwamnan ya rasu ne a Jamus a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, 2023.
Jirgin da ya kawo gawar ya iso ne da misalin karfe 3:39 na yamma, a ranar Juma’a, 5 ga Janairu.