An Dakatar Da Shugaban Wata Jami’a a Birtaniya Bisa Zargin Soyayya Da Wata Budurwa Ƴar Indiya
Daga Sabiu Abdullahi
Wata ‘yar kasuwa ‘yar Najeriya mai suna Cynthia Tooley ta taka muhimmiyar rawa wajen dakatar da Shugaban Jami’ar Buckingham, Farfesa James Tooley.
An dakatar da shi ne bisa zargin wata alaka ta soyayya tsakaninsa da wata ‘yar asalin Indiya mai shekaru 25.
Tooley ya musanta zargin, amma an dakatar da shi daga matsayinsa mai albashin fam 229,000 a shekara tun a watan Oktoba.
Rahotanni sun ce Cynthia ta mika kundin rubutun yarinyar ga mahukuntan jami’ar, wanda ya bayyana alakar da ake zargi.
Ma’auratan sun yi aure ne a watan Fabrairun 2022 bayan soyayya ta gaggawa, amma suka rabu a lokacin bazara.
Cece-kucen ya fara ne a ranar 11 ga Oktoba, lokacin da Cynthia ta sanar da jami’ar dangane da alakar da ake zargi, lamarin da ya kai ga dakatar da Tooley tare da kafa kwamitin bincike mai zaman kansa.
Lauyoyin Tooley sun bayyana zargin a matsayin “marar tushe kuma na cin zarafi,” inda suka nuna kwarin gwiwa cewa za a wanke shi.
Yarinyar ‘yar Indiya ta kare Tooley, tana mai cewa, “Ya kasance mai kirki da kulawa, kuma ya dinga girmama ni. Duk wanda ya karanta kundin rubutuna zai fahimci cewa ina son shi.”
Jami’ar Buckingham ta nada wata tawagar shugabanci ta rikon kwarya don kula da harkokin jami’ar yayin da bincike ke gudana.