December 7, 2025

An cinna wuta a wani ɓangare na fadar Sarki Sanusi

Lamido-Sanusi.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Fadar Sarkin Kano ta ba da sanarwar cewa an samu gobara a wani bangare na ginin masarautar da ke Kofar Kudu a daren Asabar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar wadda ta samu sa hannun Dan Buram na Kano, Munir Sanusi Bayero ta ce: “An samu ibtila’in wuta a fadar waje da ke fadar mai martaba sarkin Kano ta Kofar Kudu da asubahin ranar Asabar 13 ga watan Yulin 2024“.

Sanarwar ta kara da cewa “Ba a samu wata mummunar barna ba kuma babu wanda ya jikkata sanadiyyar lamarin.”

Haka nan sanarwar ta nuna cewa ana daukar duk matakan da suka dace wajen kare lafiyar wadanda ke zaune a fadar.

Tun farko, ɗaya daga cikin ‘ya’yan sarkin Ashraf Sanusi ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, wanda ya ce tun tsakar daren jiya aka cinna wutar.

Ya ce har yanzu ba a kai ga gano waɗanda suka cinna wutar ba.

Ya ce, ”Waɗanda suka cinna wutar ba a kai ga gano su ba, amma dai alhamdullahi babu wanda ya ciwo sakamakon faruwar lamarin, sannan an riga an kashe wutar da safe.”

Idan ba a manta ba, a cikin watan Mayu ne dai gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16, bayan sanya hannu kan dokar da ta yi gyara ga dokar da ta kafa masarautun Kano guda biyar ta 2019.

Tun a wancan lokaci aka ci gaba da zama cikin ɗarɗar.

35 thoughts on “An cinna wuta a wani ɓangare na fadar Sarki Sanusi

  1. Ищете бонусы для 7k Casino? Используйте промокод ANDROID777 и скачайте APK через телеграм канал https://t.me/casino_7kk

  2. Этот увлекательный информационный материал подарит вам массу новых знаний и ярких эмоций. Мы собрали для вас интересные факты и сведения, которые обогатят ваш опыт. Откройте для себя увлекательный мир информации и насладитесь процессом изучения!
    Ознакомиться с деталями – https://kapelnica-ot-zapoya-krasnoyarsk55.ru/

Comments are closed.