January 14, 2025

‘An ba wa ƴan Arewa wa’adin ficewa daga wani gari da ke Jihar Delta a Najeriya’

0
images-5-26.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Al’ummar arewacin Najeriya mazauna garin Abavo na jihar Delta, suna cikin zullumi sakamakon wa’adin kwana huɗu da ake zargin masu garin sun ba su, a kan su bar garin, tun daga ranar Litinin da ta gabata, zuwa Alhamis.

Usman Alhassan, wanda shi ne Sarkin Hausawan garin, ya faɗa wa kafar BBC cewa lamarin ya dama masu lissafi.

Ya ce, “Sun ce dole ne sai mun bar garinsu, kuma wani ma baya da kuɗin motar da zai koma gida, wasu ba su da ma kuɗin cin abinci bare na mota, kwana huɗu suka ba mu, daga Litinin zuwa Alhamis.”

A cewarsa, wannan matakin ya zamar masu babbar damuwa, saboda suna tare da iyalansu ga yara ƙanana: “Aƙalla Hausawan da ke garin nan sun kai mutum 200, muna sana’ar kayan abinci da nama, wasu kuma leburori ne.”

“Maganar ta zo daga fadar sarki, yaron sarki ne ya zo ya gaya mana, mun je domin jin ba’asi sai suka ce mana ana sace mutanensu ana neman kudin fansa, kuma suna zargin mutanenmu.”

Usman Alhassan ya ce a matsayinsa na sarkin Hausawa ba a taɓa kamo wani Bahaushe aka kawo da sunan ya aikata wani laifi ba

”Mun kai shekara talatin muna zaune garin nan, wasu Sakwkwatawa wasu Kanawa wasu kuma Katsinawa ne wasu kuma ƴan Taraba ne, muna harkokinmu muna jin daɗi, sai ga wannan abu ya zo mana bagatatan.” In ji shi, kamar yadda BBC ta ambato shi.

Limamin garin na Abavo, Malam Aliyu Yahya, ya ce suna ƙoƙarin ganin sun samu mafita, “muna kwantar wa da mutanenmu hankali, muna cewa su bi a hankali, su bi duk hanyoyin da ya kamata su bi domin samun nasara kan lamarin.”

“Mun riga mun sani cewa ko wane ɗan Najeriya yana da damar zama a ina a fadin Najeriya cikin lumana da kwanciyar hankali da zaman lafiya,”in ji liman Aliyu.

Wani ɗan majalisar masarautar garin na Abavo ya shaida faruwar wannan lamarin.

BBC ta ce Kakakin rundunar ƴansanda a jihar ta Delta, SP. Bright Edafe ya ce ba ya da labarin wa’adin da aka ba ƴan arewar, inda ya ce ya san babu wani mutum da doka ta ba damar tayar da wani ta wannan hanyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *