January 15, 2025

An ba da belin ƙananan yaran da aka kama lokacin zanga-zangar #EndBadGovernance a Kano

0
FB_IMG_1724499323224

Daga Sabiu Abdullahi   

An bayar da belin wasu yara kanana da aka kama yayin zanga-zangar #BadBadGovernanceInNigeria a kwanakin baya a jihar Kano.   

Kamar yadda rahotanni suka ruwaito, wata kungiya mai suna Advocate for Justice Alliance, karkashin jagorancin Barista AK Musa ta yi nasarar sanyawa a saki yaran.   

A baya dai rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da kama mutane 873 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a yayin zanga-zangar, inda daga bisani aka gurfanar da su a gaban alkalai tare da tsare su a gidajen yari daban-daban.   

Barista AK Musa ya tabbatar da sakin yaran, inda ya bayyana cewa, ‘’yan yara 40 ne aka bayar da belinsu daga gidan yarin Kano, babu wani babba da aka bayar da belinsa.”   

Ya kara da cewa za a ci gaba da wannan al’amari a ranar 11 ga watan Satumba, 2024, kuma kungiyarsa tana aiki da hukumar bayar da agaji ta jihar Kano domin ganin an sako wasu.   

Kamen dai wani bangare ne na murkushe masu zanga-zangar da ke neman a warware matsalar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya da kuma rashin tsaro da ake ci gaba da fuskanta. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *