An ɗage tattara sakamakon zaɓe a Kogi
Hukumar zabe mai zaman kanta ta dage tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Kogi zuwa karfe 7 na yamma ran Lahadi.
An fitar da sakamako a kananan hukumomi 18, sauran kananan hukumomi uku.
Jami’in zabe na INEC a jihar Farfesa Johnson Urama shi ne ya sanar da dage zaben.
Bayan ci gaba, za a fitar da sauran sakamakon kuma za a bayyana wanda ya yi nasara.