Amurka Ta Bayyana Shirin Sayar wa Isra’ila Makamai na Dala Biliyan 8
Daga Sabiu Abdullahi
Wani jami’in gwamnatin Amurka ya tabbatar da cewa ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta sanar da majalisar dokokin ƙasar shirinta na sayar wa Isra’ila makamai na dala biliyan takwas.
Waɗannan makaman, da suka haɗa da makamai masu linzami, bama-bamai, da sauran na’ukan harsasai, za a iya sayar da su ne kawai idan majalisar dattawa da ta wakilai sun amince.
Matakin ya zo ne ‘yan kwanaki kaɗan kafin Joe Biden ya sauka daga kujerar shugabancin ƙasar. Duk da kiraye-kirayen dakatar da goyon bayan soji ga Isra’ila saboda kashe-kashen fararen hula a yaƙin Gaza, Amurka ta ci gaba da tallafa wa ƙasar ta fuskar soji.
A watan Agusta na shekarar da ta gabata, Amurka ta amince da wata yarjejeniya ta dala biliyan 20 don sayar wa Isra’ila jiragen yaƙi da sauran kayan aiki na yaƙi.