Amotekun Ta Kama Mutum 28 Bisa Zargin Satar Mutane
Rundunar tsaro ta Amotekun a jihar Ondo ta ce ta cafke wata gungun ƴan ta’adda mai mambobi 28 da ake zargi da satar mutane da fasa-kwaurinsu.
Kwamandan Amotekun a jihar, Adetunji Adeleye, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da wadanda ake zargi a Akure, babban birnin jihar.
Adeleye ya ce wannan samame yana daga cikin nasarorin da rundunar ta samu cikin makonni biyu da suka gabata.




