Amfani da kuri’a zai fi kawo wa Najeriya maslaha sama da zanga-zanga—Kwankwaso
Jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi kira ga ‘yan ƙasar da ke shirin zanga-zangar tsadar rayuwa da su yi amfani da ƙuri’arsu wajen sauya shugabannin, maimaikon fitowa titi zanga-zangar.
Kwankwaso ya ce ƙasar ta tsinci kanta a halin matsin rayuwa da take ciki ne sakamakon kasa ɗaukar matakan da suka dace da jagororin ƙasar suka yi tun a shekarar 2007.
Cikin wata sanarwa da jagoran Kwankwasiyyar ya fitar ya ce har yanzu lokaci bai ƙure ba, na yadda za a farfaɗo da ƙasar da samar wa al’umma abubuwan ci-gaba da na walwala.
Ya ƙara da cewa hakan zai yiwu ne kawai ta hanyar samar da shugabanci nagartacce, da bin doka da kyakkyawan tsari da yin abubuwa yadda suka dace.
”Abin takaici ne yadda halayen shugabanninmu na rashin iya mulki suka jefa ƙasarmu musamman matasa cikin yunwa da rashin tsaro da fusata ta yadda har wasu daga cikinsu suka fara yanke ƙauna game da gyaruwar ƙasarmu”, in ji Kwankwaso, kamar yadda BBC ta ambato shi yana cewa.
Wasu matasan Najeriyar dai na shirin gudanar da zanga-zangar lumana ne domin nuna rashin amincewarsu kan halin matsi da tsadar rayuwa da sauran matsalolin da al’ummar ƙasar ke fuskanta.
To sai dai Kwankwaso ya zargi gwmnatin tarayya da hannu a haifar da wasu matsalolin da ƙasar ke fama da su.