Ambaliya ta kashe aƙalla mutane 60 a Brazil
Daga Sodiqat Aisha Umar
Mummunar ambaliya ta yi ajalin aƙalla mutane 60 a ƙasar Brazil.
Gwamnan Rio Grande do Sul ya ce ambaliyar ruwan da aka yi a jihar ta yi muni sosai.
Mutum 60 ne aka tabbatar sun mutu, kuma wasu dubbai sun yi ƙaura daga gidajen su bayan ambaliyar da ta taso daga gaɓar kogin Porte Alegre, babban birnin jihar.
Hukumomi sun umarci mutanen yankin su gaggauta ficewa.
Gwamna Eduardo Leite ya ce akwai buƙatar a sake gina birnin mafi bunƙasa a Brazil.
Porto Alegre, shine babban birnin jihar, da gaɓar tekun Guaiba ta ɓalle, ta kuma haddasa ambaliyar da ta kwashe duk gidajen da ke kusa.
Mutane aƙalla miliyan ɗaya ne yanzu haka, ke rayuwa a yankin mai fama da ɗaukewar lantarki, da rashin ruwan sha mai tsafta, ana kuma hasashen ci gaba da tafka ruwan sama.




