January 14, 2025

Alkali Dandago ya musanta ikirarin Sadiya Haruna cewa yana zuwa gidanta ya kwana

0
Retired-Magistrate-Muntari-Dandago.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wani babban alkalin jihar Kano mai ritaya, Muntari Dandago, ya musanta ikirarin da wata shahararriyar mai sana’r sayar da kayan ƙarfin maza, kuma ‘yar wasan kwaikwayo, Sadiya Haruna, ta yi, na cewa yakan ziyarci gidanta domin ya ci abinci kuma ya yi barci.

Ya ce ikirarin wani yunkuri ne na bata masa suna da aiki.

A watan Fabrairun 2022, a lokacin da Mista Dandago yake shugaban majistare, ya yanke wa Ms Haruna hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni shida ba tare da zabin tarar ba, bayan an zarge ta da bata wa tsohon mijinta Isa Isa suna.

Sai dai a lokacin da jarumar fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta karbi bakuncita, Sadiya ta bayyana cewa Dandago ya ci amanar ta inda ya kai ta gidan yari duk da cewa yana abota da ita.

“Abin mamaki shi ne alkalin da ya tura ni gidan yari yakan zo gidana. Mukan zauna tare, mu yi gist, mu ci abinci… Wani lokaci ma yakan kwana a gidana.  Amma a ƙarshe, abin da ya faru ke nan.  A ɗabi’a, bai kamata ya zama a cikin shari’ar ba.

“Ina jin an ci amanata saboda ban taɓa tsammanin irin wannan daga gare shi ba,” in ji ta.

Da aka tuntube shi don jin ta bakinsa, Dandago ya fada cewa zargin ba shi da tushe balle makama, ya kara da cewa yana daya daga cikin farashin da jami’an shari’a ke biya a yayin gudanar da ayyukansu.

“Ka ga, wannan wani bangare ne na kalubalen da muke fuskanta a matsayinmu na jami’an shari’a, mutane na neman tsoratar da ku ta hanyar wannan, suna tunanin za ku sunkuyar da kawunanku.

“Wannan ba shi ne karon farko da ta yi irin wannan ikirarin mara tushe ba.”

Akan aurenta da wani fitaccen jarumin nan na Tiktoker, G-Fresh Al-Amin, ta ce aurensu sa shi nai yi karko ba domin ya kasa bin sharuddan da suka amince da su kafin auren.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *