Aljeriya ta Sallami Kocinta Bayan An Kore Ta Daga AFCON
Daga Sabiu Abdullahi
A ranar Laraba ne Aljeriya ta kori kocinta Djamel Belmadi bayan da aka yi waje-rod da su daga gasar cin kofin Afrika.
Zaman Belmadi ya kare ne bayan da ya sha kashi a hannun Mauritania ranar Talata a wasansu na karshe na rukuni a Ivory Coast.
“Na sadu da kocin kasar Djamel Belmadi don tattauna abubuwan da ke tattare da wannan fitar tamu, kuma mun cimma yarjejeniya mai kyau don kawo karshen dangantakarmu da kuma dakatar da kwantiraginsa,” in ji shugaban hukumar kwallon kafar Aljeriya Walid Sadi a kan X.
Korar Belmadi ta zo ne a ranar da Ivory Coast mai masaukin baki ita ma ta kori kocinta Jean-Louis Gasset a tsakiyar gasar.




