February 10, 2025

Akwai Yiwuwar Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi

5
images-2025-01-14T143658.755.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Man fetur na iya tsada fiye da yadda ake sayarwa yanzu, kasancewar masu tashoshin mai sun kara farashi da kimanin kaso 4.74 cikin 100.

Wannan karin farashin ya biyo bayan tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, ciki har da Bonny Light na Najeriya, wanda ya tashi zuwa $80 kowanne ganga a wannan makon daga $73 a makon da ya gabata.

Vanguard ta rawaito cewa tuni wasu tashoshin mai, kamar Swift Depot, su ka kara farashin lodin man fetur zuwa N950 kan kowacce lita daga N907 kowanne lita. Tashar Wosbab ma ta kara farashinta zuwa N950 daga N909 kowanne lita.

Haka zalika, tashar Sahara ta kara farashin ta zuwa N950 kowanne lita daga N910, yayin da Shellplux ta kara zuwa N960 kowanne lita daga N908 kowanne lita.

5 thoughts on “Akwai Yiwuwar Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *