January 14, 2025

AKWAI RINA A KABA: Kotu ta ayyana zaɓen gwamnam Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba

0
WhatsApp-Image-2023-11-14-at-17.19.21_a22dc76d-e1699983001656.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Kotun daukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaben gwamnan jihar Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba.

Idan ba a manta ba, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta ayyana Dauda Lawal na jam’iyyar Peoples Democratic Party  wanda ya lashe zaben.

Ɗan takarar gwamnan jam’iyyar All Progressives, Bello Matawalle, ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen gwamnan da za a yi a ranar 18 ga watan Maris a kotun amma an yi watsi da kokensa saboda rashin cancanta.

Da ake yanke hukuncin a ranar Alhamis ne, kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba kuma kotun ta umarci INEC da ta gudanar da sabon zaɓe a kananan hukumomi biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *