January 24, 2025

Aisha Humaira ta yi alƙawarin biya wa marigayi Aminu S. Bono basussukan da ake binsa

9
FB_IMG_1700630196269.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Aisha Humaira, ta yi alkawarin biyan bashin da tsohon abokin aikinta, Aminu S. Bono, ya ciwo, wanda ya rasu a ranar Litinin.

A cikin sakon ta’aziyya da ta aike a shafinta na Instagram, Humaira ta bukaci masu binsa bashi na gaskiya da su fito, tare da yin alkawarin biyan bashin da ake binsa.

A cewarta: “Ina kira ga duk wanda yake bin Aminu S. Bono kudi ko ya sayar masa da wani abu a kan bashi kuma har yanzu bai biya ba kafin rasuwarsa da ya fito.

“Da yardar Allah zan biya bashin matukar bai fi karfina ba.

“Idan mutum yana son samun kudin tun kafin jana’izarsa, zan sauke masa dukkan nauyin da ke kansa matukar hakan bai fi karfina ba.”

Shari’ar Musulunci ta tanadar da cewa duk basussukan da ake bin mamaci ya kamata a biya masa kafin a binne su.

9 thoughts on “Aisha Humaira ta yi alƙawarin biya wa marigayi Aminu S. Bono basussukan da ake binsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *