January 14, 2025

Adadin wadanda aka kashe a Filato ya haura 100—Rahoto

0
IMG-20231225-WA0000.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

A wani lamari mai ba da fargaba, adadin wadanda suka mutu a wasu munanan hare-haren a Filato ya haura 115, in ji gwamnan jihar, Gwamna Caleb Mutfwang.

Gwamna Mutfwang, wanda ya yi magana a gidan Talabijin na Channels a ranar Talata, ya ce hare-haren ba su da tushe balle makama kuma an dora wa jami’an tsaro aikin bankado masu daukar nauyin wannan aika-aika.

“A daidai lokacin da muka kammala shirye-shiryen bikin Kirsimeti, an kai hare-haren ba gaira ba dalili a kan mutanenmu,” in ji Mutfwang.

Ya bayyana yadda wasu ‘yan ta’adda suka kai farmaki kan al’ummomi sama da 15 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar a jajibirin Kirsimeti.

Maharan sun kona gidaje da dama a daren Lahadi.

Jihar Filato dai na daya daga cikin jihohin da ke fama da rikice-rikicen kabilanci da addini.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *