April 19, 2025

‘Adadin waɗanda aka kashe a rikicin Bokkos ta Jihar Filato ya haura 70’

IMG-20231225-WA0000.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rahotanni da ke fitowa da Arewa maso Tsakiyar Najeriya na nuna cewa adadin mutanen da aka ya kai 76 a wani hari da aka kai a karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato.

A yau TCR Hausa ta yi amfani da rahotannin da suka bayyana a safiya ta wallafa cewa wadanda aka kashe sun kai 17.

To sai dai wani rahoto da BBC Hausa ta wallafa a yammacin yau ya nuna adadin ya wuce haka.

Wannan dai yanki ne da ya shahara da rikici tsakanin makiyaya da manoma.

A cewar BBC Hausa,ai magana da yawun gwamnan jihar Caleb Mutfwang ya ce gwamnati ta bayar da umarnin kama waɗanda suka kai harin domin su fuskanci hukunci.

3 thoughts on “‘Adadin waɗanda aka kashe a rikicin Bokkos ta Jihar Filato ya haura 70’

Comments are closed.