Adadin Mutanen da Suka Mutu a Hare-Haren Gaza Ya Karu da Kashi 41

Daga Sabiu Abdullahi
Wani sabon bincike ya bayyana cewa yawan mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila a Gaza ya karu da kaso 41 idan aka kwatanta da alkaluman baya-bayan nan.
Masana daga jami’ar London School of Hygiene & Tropical Medicine (LSHTM) sun ƙiyasta cewa an kashe mutane 64,260 daga 7 ga Oktoban 2023 zuwa 30 ga Yulin 2024. Wannan adadi ya zarta rahoton Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, wadda ta ce mutum 37,877 aka kashe a lokacin.
Sakamakon binciken, wanda aka wallafa a mujallar The Lancet, ya nuna cewa aƙalla kashi uku cikin ɗari na mutanen Gaza sun rasa rayukansu a yaƙin. Binciken ya kuma gano cewa kaso 59 daga cikin waɗanda suka mutu mata ne, yara, ko tsofaffi.
Masu binciken sun yi amfani da wata fasaha mai suna “capture-recapture analysis” wajen kimanta waɗannan alkaluman, tare da amfani da bayanai daga asibitoci, tambayoyi ta intanet, da kuma bayanan mutuwar da aka wallafa a shafukan sada zumunta. Alƙaluman sun nuna cewa yawan mutanen da suka mutu zuwa Oktoban 2024 ya kai sama da 70,000, yayin da Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce mutum 42,000 ne suka rasa rayukansu.”
Zeina Jamaluddine, jagorar binciken, ta ce, “Sakamakon binciken ya jaddada muhimmancin ɗaukar matakin gaggawa don tsare rayukan fararen hula da dakatar da ƙarin asarar rayuka.”
Isra’ila ta ci gaba da yaƙi a Gaza tun bayan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga Oktoban 2023. Duk da kiran Majalisar Ɗinkin Duniya na tsagaita wuta, yaƙin ya shiga shekara ta biyu, inda duniya ke yin Allah wadai da kashe-kashen da hana shigar da kayan agaji, wanda ake gani a matsayin yunƙurin kisan ƙare dangi.
Your writing is a true testament to your expertise and dedication to your craft. I’m continually impressed by the depth of your knowledge and the clarity of your explanations. Keep up the phenomenal work!SABA303
Just wish to say your article is as surprising The clearness in your post is just cool and i could assume youre an expert on this subject Fine with your permission allow me to grab your RSS feed to keep updated with forthcoming post Thanks a million and please keep up the enjoyable work SLOT DANA GOPAY
Your blog is a constant source of inspiration for me. Your passion for your subject matter shines through in every post, and it’s clear that you genuinely care about making a positive impact on your readers. SLOT DANA GOPAY
Hiya, I’m really glad I have found this info. Today bloggers publish just about gossips and web and this is actually irritating. A good web site with exciting content, that is what I need. Thank you for keeping this web-site, I will be visiting it. Do you do newsletters? Can’t find it.