November 14, 2025

Abubuwan Da Ke Kawo Cutar Kansa A Wannan Zamanin

0
cancer

Daga Muhammad Ubale Ƙiru

Zan yi gwari gwari, ba na so na cika ku da kalmomin likitanci ku ji ma baza ku iya karantawa ba. Sannan zan tsawaita rubutu amma ina gaya muku, wallahi ya cancanci lokacinku. Kuma wataƙila za ka yi da-ka-sanin ƙin karantawa nan gaba. So a yi haƙuri a karanta, minti uku ka gama. 

Jama’a kansa ta fara yawa a cikin al’umma. Shekaru goma baya “adadi” na masu kansa ♋ a Nigeria bai taka kara ya karya ba. Amma a yau ka je asibitocin koyarwa (wato Teaching Hospitals) da cibiyoyi na kansa ka ga yadda ake cincirindo a wajen. To mene ne gaskiyar magana a kan abubuwan da ke haddasa kansa? Sannan ta ya mutum zai kare kansa? Sanin kowa ne cewa kansa muguwar cuta ce, kuma ga cin kudi. So kare kanka daga kamuwa da ita ya fi komai mahimmanci a gurinmu yanzu haka.

1. Yanayin Abinci

Tabbas salon abinciccikan da muke ci yanzu sun canja sosai. Yanzu mutane sauƙi suke nema. Sannan me za a yi cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da ɓata lokacin ba. Shi ne al’amari na abincin sauri (wato fast-food) ya fito. Wato abinci da za ka iya samu a cikin kankanin lokaci. A yau, irin wadannan  abinciccikan sun haɗa da Indomie noodles, dankalin suya (Chips), Lays, Burger, Pizza, Sandwiches, kaza soyayya, Kebabs, donuts, Soda drinks da sauran nau’ikan carbonated drinks. To sannan daga wani bangaren muna da canned food irinsu Tumatur  na gwangwani, na leda, kifin gwangwani, processed food, da sauran abinci wanda ake preserving don kar ya lalace. Duk waɗannan abubuwan baza mu lazimci cinsu ba sai sun haifar mana da matsala a jikinmu. 

Shi jiki yafi bukatar abinci da aka dafa shi da kyau, kuma yake a natural form dinsa, kuma wanda artificial flavor da taste bai masa yawa ba. To sannan jiki ba ya son maiƙo da yawa, ba ya son sugar da yawa, ba ya son gishiri a yawa. Kuma ko su waɗancan  abinciccikan da na faɗa a sama ba wai ba a so ka ci su ba ne kwata kwata. A’a! Ko da za a ci, to kada su zama abincin yau da gobe. Ka ci su occasionally, lokutan events, biki, get together da sauransu. Shima kuma idan ka ci, kayi exercise don ka kone calories ɗin da ka zuba unwanted a jiki. 

2. Yanayin Tafiyar Da Rayuwa

Rashin bacci da rashin samun hutu na ɗaya daga cikin abubuwan da wasun mu har alfahari suke da su. Sai ka ji mutum yana cewa ai ni aljanijn dare ne. Ba na bacci, bai fi na yi baccin awa biyu ba na tashi. Sannan ni mai aiki tukuru ne. Ba na son hutu, ba na son zama waje ɗaya. A shekara ba na hutu sama da na kwana uku ko biyar. To maganar gaskiya wannan ba abin birgewa ba ne ko abin cinyewa. Rashin bacci yana da illa sosai a kan sauran sassan jiki. Ko kwamfuta ta there was a time da nake barinta a kunne non-stop for 7 days. Wallahi idan ban yi restarting ba sometimes ba ta aiki da kyau ballantana mutum. ƙwaƙwalwarka tana buƙatar hutu, kuma Allah da ya sanya mana bacci a cikin rayuwar mu ya san mahimmacinsa shi ya sa ya bamu. Daga cikin illolin rashin bacci akwai karya garkuwar jiki, sannan akwai  tabin hankali, sannan akwai rashin bacci baya baiwa jiki damar yayi repairing damages cells da DNA. Wanda sune eventually suke forming sai su zama kansa. Shi yasa masu hikima suke cewa idan ka kalli rayuwar dabbobi, kare ba ya tsawon rai kamar tinkiya. Saboda shi kare ba ya bacci, ita kuma tinkiya bacci gareta. 

3. Magungunan Ƙayyade haihuwa

Akwai labaruka marasa daɗi da zarge zarge masu karfi akan contraceptives na zamani especially allura da kuma implant, although babu research officially da ya tabbar da haka, yawanci an samu bayanai ne daga mutane wanda suka sanya abubuwan ƙididdige haihuwa wato family planning. Bayan fara amfani da su, sai suka ga canje canje a jikinsu, wanda shine sila na fara samun kansa a jikinsu. Misali daga cikin kansa da ake zargin wannan contraceptives tana sakawa shine kansa mahaifa, kansa nono, kansa ciki da sauransu.

Wannan yasa ake bada shawara da a yi dogon nazari sosai a kan irin kariyar da za a yi amfani da shi. Misali hanya mafi sauki kuma mara illa ita ce namiji ya koyi inzani wato withdrawal method. Idan yaji zai releasing sai ya cire. Duk da dai cewa wasu basa iyawa kuma idan aka samu kuskure zai iya kawo abinda ba’aso. Amma dai akwai Youtube videos da dama akan yadda namiji zai training kansa a kan inzani.

4. Kayan mata

Without a doubt, bincike na ilimi ya tabbatar da cewa kayan mata suna haifar da kansa. Anan me ake nufi da kayan mata? Kayan mata shi ne duk wani abu da mace za ta cusa a farjinta don ta ƙara ni’ima ko daɗi kamar yadda ake faɗa, ko kuma wani abu da za ta sha don ta ƙara girman Rufaidah Yogurt ɗinta ko kuma mazaunanta, ko kuma don ƙara ƙiba ko rage ƙiba. A nan zan yi adalci ga wasu masu maganin kayan matan. Tabbas suna hada sinadarai ne daga cikin sanannun abubuwa wanda kowa ya sani. Misali haɗin kankana, dabibo, aya, ayaba da sauransu a matsayin abin sha don ƙara wa mace ni’ima. Amma akwai azzaluman mutane wanda ba su da ilimi kawai neman kuɗi ne a gabansu. Zama suke su yi haɗe haɗe sometimes har da ƙwayoyi, ko kashin dabbobi, ko maniyin kare, wato sperm ɗin wata dabba, ko magunguna da ake baiwa dabbobi, ko maganin bacci da maganin cin abinci. Sai a hada su waje guda mutum ya sha ya rika bacci kamar dabba wai don ayi manipulating metabolism na jiki don a yi ƙiba ko don a cimma wata buƙata. Wannan duk shirme ne yana haifar da kansa ta bakin mahaifa, kansa farji, kansa ciki, kansa jini, kansa nono da sauransu. Sannan har wa yau akwai suppliments da wasu suke sawa a musu a kasashen waje irinsu india, bangaledash da sauransu don su kawo nan su sayarwa da mutane. 

Mun faɗa da babbar Murya a kiyayi supplements❗

Duk ba a ce kar ayi gyaran ciki ba, amma akwai abubuwa da aka tabbar da ingancinsu wanda suke ƙara ni’ima da kyan jiki. Su suka fi dacewa da mace ba wani kwashe kwashe da ake sayar muku online ba. Wata ma har abada idan ta cuceka baza ka ganta ko ka san inda take ba. Don haka a kula. In fact ma dai babu wani Abu da private part na mace yake bukata da ya wuce iya tsarki Shi kanshi,eh ki iya tsarkake gurin tare da bambancewa tsakanin tsarkin fitsari da na bayan gida.

  A Fara tsarkake gurin fitsari sannan a yi tsarkin bayan gida a Kula.

  Wannan gurin Shi yake tsaftace kanshi ba ya buƙatar sabulu ko omo akwai wani ɗan fluid da ke fitowa time to time to wannan Shi ne yake tsarkake gurin tare da ba Shi kariya daga cutuka.idan ma akwai abinda za ki yi to Kada ya wuce tsarki da ruwan ɗumi ba kuma ruwan zafi ba a’a ruwa mai ɗumi domin Idan zafin ruwan ya yi yawa Shi ma zai yi wa ƙwayoyin halittar da ke gurin illa Wanda su kuma Allah ta’ala ya haliccesu ne don su yi gadin gurin.

      Cusa magani ko wane iri ne a wannan gurin risky ne ga lafiyarki,a Kula Idan ba maganin infection aka Baki ba irinsu Nystatin ovules da sauransu Kada a yi matsi da komai akwai nau’ikan exercises da za ki yi don tsokokin gurin su matse ba tare da kin siyo cuta da kudinki ba.

5. Kayan  Shafe Shafe da Adon Mata

Na san da mata sun zo nan gaɓar za su ce wallahi ƙarya ne ba a isa ba 😁 . To a yi haƙuri a karanta, gaskiya ɗaya ce. Kun ga kayan makeups, lotions, skin bleaching, shafe shafen abubuwan gyaran fata. Wallahi su ma manyan agents ne wajen causing kansa. To amma meye alaƙarsu da kansa? Alaƙar ita ce. Ita fata naturally tana da ƙofofi, kuma ɗaya daga cikin aikin da ƙofofin suke yi shi ne absorbing Vitamins irin su Vitamin D. Idan ƙofofin fata suka suki Vitamins suna kai su cikin jini don baiwa jiki wannan nutrient ɗin. To idan kika shafa Makeup ko Man bleaching, ko man gyaran fata, a maimakon ƙofofin fata su  zuƙi vitamins, sai su tarar da makeup and creams sun rufe fatar. Shikenan sai su dauka su kai cikin jini, daga nan sai jini ya kai su Liver, Kidney, heart da sauransu. Shikenan bayan tsawon lokaci sai kansa ta yi manifesting.

6. Kayan Maye da Bugarwa

Babu ko ja akai masu shaye shaye suna fuskar barazana ta kansa a kowane second na kowane minti na rayuwarsu. Mu fara da kayan hayaƙi. Sune number agent da suke causing lung kansa, throat kansa da mouth kansa har ma da breast kansa. Kuma kayan hayaƙi sun haɗa da taba sigari, wiwi, vaper, waza, da sauransu. Bangaren abubuwan sha irinsu kodin, cali, cocain, alcohol, su kuma sune suke haifar da kansa ta koda, hanta, breast kansa, pancreatic kansa, da sauransu. So, ɗaya daga cikin dalilin yawaitar kansa yanzu a cikin wannan al’ummar tamu akwai shaye shaye. Mata na yi maza na yi. Wannan ya sa statistics ɗin kullum suke ƙara sama. 

7. Kayayyakin Leda Da Goruna (Plastic Product)

Kun ga ledar pure water da waɗannan robobin na lemuka, su ma akwai wasu chemical a jikinsu wanda ake kira Bisphenol-A da Phthalates. A duk sanda aka ajiye leda ko roba ta dauki tsawon lokaci da abu a ciki, wannan chemicals ɗin suna zagwanyewa su koma su gauraya da Ruwan ko lemun. Idan mutum ya sha sai su haifar masa da kansa a jikinsa. 

So don kare kai ba a so a riƙa ajiye su a inda rana zata dake su. Sannan kar ka ga ruwa a Traffic junction kawai ka saya ka sha. Sannan idan da hali idan za’a sha Ruwan leda a rika juyewa  cup kafin a sha. 

8. Gamuwa Da Radiyeshan (Radiation)

Wannan shi ya fi damu na domin ko wane ɗaya daga cikinmu yana cikin risks ɗin kamuwa da kansa ta wannan hanyar. Kun ga smart phones, Ear Bluetooth devices, Head phone, Smart watch, smart TV, electronics, Cooking Oven, Washing machine, WiFi Routers, etc. Duka wadannan abubuwan suna emitting abin da ake kira radiation. Shi radiation wani sinadari ne na energy da yake yawo a sararin sama wanda idan ba’a kula ba contact da shi ta hanyar wadannan abubuwan zai iya damaging cells, DNA, sannan ya kuma haifar da uncontrolled growth na cells wanda shine kansa din. Nau’ikan kansa da radiation yake sakawa sun haɗa da  leukemia, brain tumors, and breast kansa. 

Duk da cewa yanzu we cannot do without waɗannan abubuwan, amma za mu iya ragewa. Misali kar ka riƙa kawo wayarka kusa da jikinka, ka rika amfani da Hands-free fiye da karawa a kunne. Sannan kar a riƙa dumama abinci da micro-wave. Sannan kar a riƙa mu’alama ta kusa da kusa da waɗannan gadgets din. 

9. Matsalolin Muhalli

Babu makawa muna rayuwa a cikin wasu abubuwa da suke cutar da mu ba tare da mun gane ba. Kunga makotaka da industrial zones wato unguwanni da suke da kusanci da masana’antu yana da matukar hadari ga lafiya. Misali anan Kano muna da Sharada Industrial area. Zaka ga hayaki da yake fitowa daga cikin masana’antun, sannan ga chemicals da suke zubarwa a kasa yake komawa cikin ruwa. Sannan ga hayakin motoci da hayakin bola da ake saka wa wuta. Duka waɗannan suna haifar da kansa na huhu wato Lungs kansa. Sannan uwa abu suna affecting jarirai da ma ba’a haifa ba. Zaka ga yaro yazo duniya da rashin lafiya ko wata nakasa a jikinsa sakamakon wannan effects din na environment. 

10. Lafiyar Mutum Ta Zahiri

Babu makawa rashin motsa jiki yana daga cikin causal agents na kansa. Domin prolonged inactivity wato ka dade baka motsaba ya causing slow metabolism wato jinkiri wajen sarrafa abinci har ya shiga cikin jini. Hakan yana haifar da colon kansa har ma da breast kansa. 

Hanyoyin magance hakan shi ne mutum ya kasance mai motsi a kowane lokaci. Kar ka zauna ka yi awanni a zaune waje ɗaya ba tare da ka motsa ba. Duk inda ka yi awa a zaune to ka tashi ka ɗan yawata sai ka dawo ka zauna. Sannan idan ka ci abinci kada kawai ka zauna guri daya. Tashi ka ɗan yi tafiya ko da ta minti goma ne. Sannan aƙalla ka motsa jiki ko da na minti talatin ne  a cikin sati sau uku. Motsa jiki yana nufin ko tafiyar kafa, hawa bene da sauransu.

11. Dumamar Yanayi

Mutane da yawa suna underestimating tasirin ɗumamar yanayi (dumamar yanayi)  akan lafiyar al’umma. Mutane irinsu Donald Trump na daga cikin shugabanni da su kayi watsi da warning din da ake bayarwa akan dumamar yanayi. Alakar dumamar yanayi da kansa shine a sararin sama wato atmosphere da turanci, akwai wata shimfida da Allah ya shimfida wacce ake kira da suna Ozone Layer. Wannan shimfida ita take hana radiation (wato yayan rana masu cutarwa) shigowa cikin sararin duniyar mu. Shigowarsa yana haifar da cututtuka irinsu skin kansa, da sauran nau’ikan kansa da ake fama dasu. Kuma shi wannan GW yana assasa air and water pollution. Shan polluted water da shakar polluted air yana kawo kansa kala kala. 

So daga yanzu idan kana kona bishiya ko sareta, ko kona bola, ko idan ka rufe kanka a mota kana shan AC ko ka kunna kwamfuta tun safe har yamma, to ka tina cewa ɗumamar yanayi is forming. Hanyar magance shi ta farko shine shuka bishiyu da rage kone kone da lalata environment. Ta haka ne kadai zamu rage spread  na kansa. Kuma wannan aikin ba namu bane kadai, dole sai gobnati na shigo. So a daina sare bishiyu.

🎗Hanyoyin Kariya daga kansa

1. Cima

Akwai statistics da suke nuni da cewa mutanen kasar China da India suna daga cikin jinsin mutane da suke da karancin cutar kansa kuma life expectancy nasu yake da girma. Masu binciken suka ce, mutanen kasashen biyu suna kokari sosai wajen cin abinci mai kyau. Nau’ikan abinci da suka fi shahara a wajensu sun hada da 

🌿- Amfani da vegetables sosai a cikin abinci irinsu broccoli, Cauliflower, Moringa wato Zogale, Spinach wato alayyahu da kuma bitter leaf. 

🍎 – Bangaren fruits, suna amfani da berries wato inibi, orange wato lemo, da kuma lemon tsami. Aka ce lemon tsami yana da tasiri sosai a kan ƙwayoyin halittar cutar kansa. 

🧄- ɓangaren Spices da Herbs aka ce suna amfani da Turmeric sosai da kuma garlic da Onions, da kuma ginger. Wadannan abubuwa ne da ake samu  har a cikin magungunan kansa din su kansu. Fara amfani da su a yau da gobe zai preventing kansa insha Allah. Sannan akwai irinsu Green Tea, Black tea, Pepper mint, Black pepper da Habbatus-sauda, da sauransu. Duka suna da magunguna a cikinsu.

   Kun ga man habbatus-sauda wato antibiotic ne in ji masana,suka ce Idan za Ka juri Shan tea spoon safe da yamma in sha Allahu jininka zai Zama fresh kuma jininka zai tsira da kamuwa daga miyagun cutuka irinsu kansa din,sannan duk wasu infections da Ake fama da su a Cikin ciki da hanji to Kai Ka tsira daga sharrinsu.

💧- Sannan babban magani kuma makami wanda muka fi rainawa shine ruwa. Ruwa abokin aiki, Ruwan maganin kowacce irin cuta. Shi ruwa shan sa da yawa yana flushing out toxins wato gurbataccen abinci da kuma cuta da ke jikin ɗan adam. Kuma mutane ba sa son shan ruwa. Ni a zamana da Indians da Chinese idan akwai wani abu da na koya to shan ruwa ne da cin albasa da garlic. Basa rayuwa babu su. Kuma duk abinda kake da gorar ruwanka tare da kai. Wadatancen ruwa da ake so ɗan adam ya sha shi ne 3-4 litres a rana. 

2. Dabi’a da yanayin rayuwa 

🏋- Maganar exercise wato atisaye ba kawai magana ce ta motsi ba. A’a, exercise yana taimakawa wajen bunƙasa garkuwar jiki, kare jiki daga cututtuka, hana cuta samun wajen zama, sannan yana kore stress da gajiya. Sannan uwa uba, exercise yana hana tsufa da wuri za Ka ga jikinka Yana kyau kuma fatar jikinka ba za ta dinga yamushewa ba, rashinsa kuma yana kawo tsufa kusa kusa Idan kana da shekara arba’in sai a dinga yi maka kallon Mai shekara saba’in. 

🥗- Cin abinci mai kyau kamar yadda na faɗa a sama, da kuma ƙayyade cin abinci. Ci da yawa a lokaci guda yana haifar da matsaloli da dama including slow metabolism. Ana so idan za ka ci abinci ka rarrabe. Maimakon ka ci duka lokaci guda, zaka iya ci sau biyu ko sau uku bayan wasu intervals. Sannan yana da kyau ka riƙa azumi. Azumi na Litinin da Alhamis bayan lada yana da medical benefits, yana baiwa ciki damar adjusting metabolic reactions and processes. 

😴 – Samun bacci wadatacce shima key factor ne. Wadataccen bacci shi ne ka kwanta da wuri, ka samu aƙalla baccin awa shida ba tare da kana tashi kana komawa ba. Idan kai me tashi ibadane, to ka rika kwanciya karfe 10 na dare. Ka tashi ƙarfe 4am na dare ka yi ibada shikenan ka gama. Wannan shine baccin masu kudi idan baka sani ba. Da Bill Gates da Elon Musk da masu kudi da yawa wannan shine routine din baccinsu. 

🌞 – Amfani da natural abubuwa akan artificial. Duk abinda kirkirarsa akai kamar kayan abinci, ka yi avoiding. Sannan ka riƙa fita wajen gari time to time kana shan natural iska. Sannan ka rika kallon korayen bishiyu da green environment. Zai taimakawa jikinka sosai. 

  Yawan kallon korayen ganyaye da sanyin safiya Yana ƙara lafiyar idanu in ji masana.

🧘- Sannan yaki da damuwa da kuma minding business Dinka akan abubuwa yana increasing lafiyar jiki. Saka hassada da mugunta a zuci da yawan damuwa suna cutar da jiki, kuma mutum yana tsufa da wuri kuma ya rasa focus. Avoiding rana yana da mahimmaci, idan za’a fita.

Zai fi kyau a kiyaye yawan Shiga Cikin zafin Rana Mai tsananin quna…a fita da sanyi safiya ko da hantsi,ko kuma a fita da sanyin marece.

💊- Avoiding drug abuse, wato amfani da magunguna ba tare da umarnin likita ba. Shima yana kawo mutuwa organs na jiki da haifar da kansa. 

Conclusion

A karshe bincikena da alƙalumman  masu bincike sun tabbatar da cewa kula cima da lifestyle na mutum suna preventing faruwar kansa da more than 80%. Sannan yanayin yadda muke mu’amalantar environement dinmu ma yana taka rawar gani sosai wajen kore ko samar da cutar kansa a cikin al’umma. Ita kansa dadinta shi ne kar ta kama ka, amma da zarar ta kama ka to zance ya kare sai ta Allah kawai. Recovery rate nata is very low, kuma har yanzu ba a san takamaimai mene ne maganinta ba. Don haka riga-kafi  ya fi magani in ji masu iya magana. 

Daga Muhammad Ubale Kiru

13th Nov 2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *