ABIN TAUSAYI: An yanke wa wata yarinya ƴar shekara 13 hannu mai suna Fauziyya Sani sakamakon rashin kuɗin kai ta asibiti a jihar Zamfara

Daga Comr Nura Siniya
Matuƙar kana raye ba a gama halittar ka ba har sai ka koma ga Allah
Wannan yarinyar da kuke gani sunanta “Fauziyya Sani, ta haɗu da tsautsayi a satin da ya gabata sakamakon faɗowa da tayi daga kan gado wanda hakan yasa ta samu karaya a hannu wanda sanadiyyar haka ne ya sa aka gutsure mata hannu sakamakon rashin kuɗi da iyayenta suke fama da shi a jihar Zamfara.
A zantawar da gidan talabijin na yanar gizo Mai-Biredi Tv suka yi da Fauziyya ta bayyana cewa tun farko ɗaurin gida ne da aka yi mata wanda hakan yai sanadiyar riƙe mata jijiyoyin hannu wanda yasa jini baya motsawa.
A cewar Fauziyya ta kammala karatunta na firamare tsawon shekara 3 da ta wuce amma har yanzu bata samu damar cigaba da karatu ba saboda rashin kuɗi har bayan faruwar wannan jarabawar da Allah yai mata, inda tace tana son ta cigaba da karatu idan ta samu wanda zai taimaka mata.
Allah Ya raba mu da mummunar ƙaddara ya bata ikon cinye wannan jarabawar ya kuma bata lafiya.
