Abin fashewa ya raunata kananan yara 10 a Kaduna
Daga Sabiu Abdullahi
Kidandan, karamar hukumar Giwa, jihar Kaduna, ta fuskanci tashin hankali da yammacin ranar Asabar lokacin da wani abin fashewar ya jikkata kananan yara 10.
Lamarin ya faru ne yayin da suke wasa da wani abu da aka gano a wani daji da ke kusa, wanda ake zargin bam ne.
Hotuna masu tayar da hankali da ke yawo sun bayyana wadanda abin ya shafa a cikin jini yayin da mazauna yankin suka yi gaggawar ba da agajin gaggawa.
Daga baya an kai yaran da suka jikkata zuwa Asibitin Shika da ke Zariya don samun kulawar lafiya.
Shugaban ƙauyen Alhaji Abubakar Umar Ruka ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa, “mutane 10 sun jikkata, kuma ba a samu rahoton mutuwarsu ba. An kai su asibiti domin yi musu magani, kuma a halin yanzu ina hada sunayensu.”
‘Yan sanda sun ziyarci wurin don gudanar da bincike kan lamarin.