Abdul Ningi ya dawo Majalisar Dattijai bayan dakatarwar wata 3
Daga Sabiu Abdullahi
Sanata Abdul Ningi mai wakiltar mazabar Bauchi ta Tsakiya ya koma zaman majalisa a yau Talata, wanda ya kawo karshen dakatarwar da aka yi masa na tsawon watanni uku.
Majalisar dattijai ta yi afuwa tare da tuno da Ningi, nan take, biyo bayan kudirin da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro ya gabatar a makon jiya.
Moro ya bayyana nadama a madadin Ningi kuma ya dauki alhakin abin da ya aikata.
Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, ya sanar da dawo da Ningi ba tare da wani sharadi ba bayan rokon wasu ‘yan majalisar.
An fara dakatar da Ningi ne a ranar 12 ga Maris, 2024, bayan wata tattaunawa mai cike da cece-kuce inda ya yi zargin cewa an samu sabani a cikin kasafin kudin 2024, inda ya ce majalisar ta amince da N25tn yayin da fadar shugaban kasa ta aiwatar da N28.7tn.