Abba da Gawuna: Yau kotu za ta yanke hukuncin taƙaddamar zaɓen Kano
Daga Sabiu Abdullahi
Kotun Daukaka Kara ta Abuja, ta sanya ranar Juma’a 17 ga watan Nuwamba, 2023, domin yanke hukunci a kan rikicin zaɓen gwamnan jihar Kano tsakanin Gwamna Abba Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, da Nasiru Gawuna na jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
A wata sanarwa da kwamitin kotun ɗaukaka kara ya fitar, za a yanke hukuncin ne da karfe 10 na safe, a halin yanzu, gwamnatin jihar Kano ta buƙaci da a kwantar da hankali gabanin yanke hukunci kan zaben gwamnan.
A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya fitar, gwamnatin ta bukaci magoya bayan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da su kwantar da hankalinsu tare da kauce wa duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ruɓanya kokarinsu wajen tabbatar da doka da oda da kuma zaman lafiya a jihar domin wasu masu aikata miyagun laifuka na son cin moriyar lamarin.