May 16, 2025

A Yi Hattara: Yadda Matasa Za Su Kauce wa Sharrin Damfarar Aikin Bogi a Najeriya

images - 2025-04-19T093231.804

Daga Sabiu Abdullahi

A halin yanzu, matsalar damfarar aikin bogi na kara yawaita a Najeriya, inda masu damfara ke amfani da hanyoyi daban-daban wajen yaudarar matasa da fatan samun aikin yi.

Wannan matsala ta janyo asarar kudi da lokaci ga dubban matasa, wasu ma sun fada cikin hadarin rayuwa.

Don haka, wannan rubutu na TCR HAUSA zai bayyana yadda matasa za su gane irin wadannan damfara da kuma yadda za su kare kansu.

1. Ka Guji Kamfanonin Da Ke Neman Kudi Kafin Su Dauke Ka Aiki: Wata hanya mafi shahara da masu damfara ke bi ita ce neman a biya wani “kudin rijista”, “kudin horo” ko “kudin uniform” kafin a fara aiki. Dole ne matasa su sani cewa sahihin kamfani ba zai bukaci kudin wani abu kafin daukar ka aiki ba.

2. Yi Bincike Sosai Game da Kamfanin: Kafin a amince da kiran aiki, yana da kyau matashi ya bincika kamfanin a yanar gizo ko ya tambayi wadanda suka taba jin sunansa. Idan kamfanin ba shi da adireshi tabbatacce ko kuma ba a iya samun wani bayani a kansa, to akwai yiyuwar damfara ce.

3. A Guji Shiga Abu Marar Tabbas: Wasu masu damfara suna ɓoye kansu a matsayin ‘yan kasuwa ko kamfanonin tallace-tallace, amma da zarar an fara “aiki”, sai a gane cewa ana amfani da kai ne wajen yawo a gari kana karbar kudi daga mutane a hanyar da ba ta dace ba.

4. Kar a Damu da Gaggawar Samun Aiki Ta Kowanne Hali: Idan wani yana matsa maka ka gaggauta turo bayananka ko kudin wani abu domin kada ka rasa aikin, to ka dauka cewa akwai abin da ake boyewa. Kamfanoni na gaskiya suna da tsarin daukar aiki mai tsari, ba wai na gaggawa da rudani ba.

5. Ka Kiyayi ‘Text Message’ Ko ‘Email’ Marasa Bayani Cikakke: Wasu masu damfara na aiko da sakonni na karya da suna na manyan kamfanoni, suna bayar da lambar waya kawai ba tare da adireshi, lambar lasisi, ko sahihan hanyoyin sadarwa ba. Wadannan yawanci ba su da tushe balle makama.

6. Ka Tuntubi Masana Ko Hukuma: Idan ka samu tayin aiki da kake da shakku a kai, yana da kyau ka nemi shawara daga kwararru ko kuma ka kai korafi zuwa ofishin hukumar da ke yaki da damfara kamar EFCC, ICPC ko ma ‘yan sanda.

Yin hattara da wayar kai suna daga cikin makaman kare kai daga fadawa tarkon masu damfara. Aikin yi na gaskiya yana zuwa ne da hakuri, da neman Allah da kuma kokari. Kada fatan samun aiki cikin sauki ya jefa ka cikin hadari.