‘A idon gwamantin Buhari aka kashe mutane sama da 60,000 amma bai yi komai a kai ba’—Shehu Sani
Daga Sabiu Abdullahi
Tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya caccaki tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya zargi gwamnatinsa da taimakawa wajen tabarbarewar tsaro da ba a taba ganin irinsa ba.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne a shafin sa na X (watau Twitter) a ranar Lahadi.
Shehu Sani wanda wa wakilci Kudancin Kaduna, ya zargi masu ruwa da tsaki na Arewa da yin shiru duk da yawan kashe-kashe da aka yi a lokacin gwamnatin Buhari.
Ya ci gaba da cewa ’yan Arewa da suka samu dama kwatsam sai suka yi shiru tsakanin 2015 zuwa 2023 saboda tsohon shugaban kasa dan Arewa ne.
Dan gwagwarmayar ya ce adadin wadanda suka mutu a cikin shekaru takwas na gwamnatin Buhari ya kai 63,111.
Rubutun nasa ya kara da cewa, “Da yawa daga cikinsu sun yi shiru, sun kuma amince da zubar da jini da garkuwa da mutane a Arewa tsawon shekaru takwas.
“Sun kira mu da sunaye iri-iri a kokarinsu na kare gazawar. Sun yi biris da gawarwakin ’yan uwansu, sun fi sha’awar kare Shugabansu.
“Sun yi shiru lokacin da aka kashe mutane kusan 63,111; An yi garkuwa da su sau biyu, ciki har da dalibai 1,680.