June 14, 2025

Ƴansanda sun daƙile yunkurin yin garkuwa da wasu mutane a Abuja

image_editor_output_image1265413120-1719817815895.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan Abuja da ke yaki da masu garkuwa da mutane ta yi nasarar kubutar da wasu mata biyu, Mart Ojadi mai shekaru 15 da Evelyn Chinaza mai shekaru 12 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a kauyen Guto da ke Bwari a ranar 30 ga watan Yunin 2024.

A cewar wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, SP Josephine Adeh ya fitar, rundunar ‘yan sandan tare da hadin gwiwar jami’an DSS, sun bi sawun masu garkuwa da mutanen zuwa dajin Gauraka na jihar Neja, inda suka yi ta artabu da su, wanda ya tilastawa masu gudu da raunuka.

An kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su ba tare da samun wata matsala ba, kuma tuni aka sake hada su da iyalansu.

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, CP Benneth C. Igweh, ya jaddada aniyar rundunar na wanzar da zaman lafiya da tsaro a babban birnin kasar nan.

1 thought on “Ƴansanda sun daƙile yunkurin yin garkuwa da wasu mutane a Abuja

  1. I am genuinely thankful to the owner of this website for sharing his brilliant ideas. I can see how much you’ve helped everybody who comes across your page. By the way, here is my webpage UY8 about Thai-Massage.

Comments are closed.