January 14, 2025

An kama wata mata da ake zargin ta caka wa mijinta wuka har lahira a Yobe

1
IMG-20240613-WA0004.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Jami’an ‘yan sanda a jihar Yobe sun kama wata matar aure mai suna Zainab Isa ‘yar shekara 22 bisa zargin kashe mijinta mai suna Ibrahim Yahaya mai shekaru 25 a Damaturu babban birnin jihar.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, lamarin ya faru ne biyo bayan wata sa-in-sa a unguwar Abbari, wanda ya rikide zuwa faɗa na zahiri.

“Rundunar ta na bakin ciki da rashin tausayin abin da wasu ma’aurata suka aikata wanda ya kai ga mutuwar wani matashi mai a dalilin rashin jituwa tsakaninsu,” in ji Abdulkarim.

Wadda ake zargin ta amsa ta aikata haka me don kare kanta a lokacin da ta yi mata dukan tsiya, inda ta ce ba ta da niyyar kashe shi.

Ma’auratan sun haifi ɗansu na biyu ne a farkon watan Yuni, kuma Zainab na ci gaba da samun sauki sakamakon tiyatar da aka yi mata a kwanan baya.

1 thought on “An kama wata mata da ake zargin ta caka wa mijinta wuka har lahira a Yobe

  1. Whenn I initially comented I clicked the “Notify me when new comments are added” checkbox andd now each ttime
    a comment is adderd I get seeral emaios with
    thee same comment. Is there any way yyou can rermove people from tha service?
    Thanks!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *