May 17, 2025
FB_IMG_1719329070603.jpg

Wani lamari ya afku a majalisar dokokin tarayya da ke Abuja ranar Talata, yayin da wani babban jami’in hukumar kwastam ta Najeriya ya fadi ya mutu a zaman da kwamitin asusun gwamnati na majalisar wakilai ke yi.

Ma’aikacin kwastam din wanda ba a bayyana sunansa ba ya rasu nan take a ranar Talata bayan ya yanki jiki ya fadi yayin amsa tambayoyi a ci gaba da gudanar da bincike kan hukumomi masu samar da kudaden shiga da kuma ma’aikatu.
 
Mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi, ya sanar da rasuwar jami’in kwastam din, inda ya ce, “Abin bakin ciki da nadama ne muka tabbatar da rasuwar wani jami’in hukumar kwastam ta Najeriya wanda ya kasance a majalisar dokokin kasar domin ganawa da kwamitin majalisar.

3 thoughts on “

Comments are closed.