2027: Ban ce zan zama mataimakin shugaban ƙasa ga kowa ba—Peter Obi

Daga Sabiu Abdullahi
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya bayyana matsayinsa kan zaben 2027, inda ya bayyana cewa bai taba cewa zai yarda ya zama mataimakin shugaban kasa ga kowa ba.
Obi ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, bayan wata hira ta musamman da New Central TV, wanda ya yi ikirarin cewa an yi masa mummunar fassara.
A cikin hirar, Obi ya ce: “Idan na ga mutanen da za su iya yin aikin da kyau, zan (iya da zama mataimakin shugaban kasa).”
Duk da haka, a yanzu ya yi iƙirarin cewa “maƙiya ne suka murguda kalamansa ta hanyar yin farfaganda.
Obi ya jaddada kudirinsa ga jam’iyyar Labour da kuma burinsa na ciyar da Najeriya gaba.
Ya yi nuni da cewa ba ya burin zama shugaban kasa ta kowane hali amma ya kuduri aniyar ganin Najeriya ta ci gaba.
Ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya yi aiki da wasu da suke da ra’ayinsa, amma ba tare da wadanda kawai burinsu shine kama jihar ko cin zabe ba.