Ƴan Bindiga Sun Nemi Naira Miliyan 150 Don Sakin Daraktocin Ma’aikatar Tsaro Da Suka Sace A Kogi
Sabbin bayanai sun bayyana game da sace daraktoci shida na Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya, inda masu garkuwar suka bukaci N150m a matsayin kudin fansa.
An sace jami’an ne a ranar 10 ga Nuwamba, 2025, a kan hanyar Kabba–Lokoja a jihar Kogi, lokacin da suke tafiya daga Legas zuwa Abuja domin halartar jarabawar karin matsayi.
Majiyoyi sun ce ’yan bindigar sun yi wa tawagar su zagon-kasa, suka toshe hanyar sannan suka yi awon gaba da su.
Wani dan uwa na daya daga cikin wadanda aka sace ya bayyana matsananciyar damuwa game da bukatar kudin fansar.
Kungiyar ma’aikata ta ASCSN, a cikin sanarwar da Shugabanta, Shehu Mohammed, da Sakataren Janar, Joshua Apebo, suka rattabawa hannu, ta la’anci sace-sacen.
Kungiyar ta tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin ganin jami’an sun kubuta lafiya.
ASCSN ta bayyana sunayen wadanda aka sace da suka hada da Mrs Ngozi Ibeziakor, Mrs C. Emeribe, Mrs Helen Ezeakor, Mrs C. Ladoye, Mrs J. Onwuzurike, da Mrs Catherine Essien, dukkansu manyan ma’aikata ne na Command Day Secondary School (CDSS), Ojo, Legas.
Kungiyar ta ce Ma’aikatar Tsaro ta riga ta hanzarta daukar matakai tare da hukumomin tsaro da sauran bangarori domin gaggauta ceto su.
Iyalai da abokan aikin wadanda aka sace na fatan kokarin da ake yi zai kai ga sake su lafiya.




