January 14, 2025

Ɗansandan da ya shawu ya kashe mahaifinsa har lahira a Borno

10
Nigerian-police-750x414.webp

Daga Sabiu Abdullahi

Wani dan sanda Sajan ya harbe mahaifinsa, ASP Wadzani Ntasiri, wanda ya kasance mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP) mai ritaya, bayan wani artabu da aka yi ranar Lahadi a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ɗn sandan wanda aka bayyana sunansa a matsayin Linus Wadzani, ma’aikacin ‘yan sandan tafi da gidanka ne da MOPOL 6 Maiduguri, kuma yana aiki a matsayin jami’in tsaro a harabar majalisar dokokin jihar Borno. 

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin a hedkwatar rundunar ‘yan sandan jihar da ke Maiduguri, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), ASP Nahum Daso, ya ce mahaifin dan sandan da ya kashe shi ya yi aiki da rundunar jihar kafin ya yi ritaya.

Da yake ba da labarin lamarin, PPRO ya ce Sgt Linus ya isa gida da misalin karfe 4:30 na yamma kuma sun tafka kazamin fada da mahaifin wanda ya kai shi harbin mahaifin sau da dama da bindiga kirar AK47 wanda ya kai ga mutuwarsa nan take.

10 thoughts on “Ɗansandan da ya shawu ya kashe mahaifinsa har lahira a Borno

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *