November 10, 2024

Ɗan Tseren duniya Kelvin Kiptum ya mutu

0

Daga Mustapha Mukhtar

Kelvin Kiptum ɗan asalin kasar Kenya ya mutu sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi da kocinsa Gervais Hakizimana dan ƙasar Rwanda.

Mutumin mai shekaru 21 ya rasu ne a ranar 11 ga watan Fabarairu shi da kocin nasa sakamakon hatsarin mota, wanda likitan gwamnati ya tabbatar da buguwa ne a kai ya kashe matashin ɗan tseren.

Mutuwar tasa ta faru ne bayan lashe gasar da ya yi ta tsere ta rukunin maza da ta gabata a Chicago a kwanan baya, wanda ya lashe gasar a awa 2 da sakwan 35.

Ana sa ran zuwan Shugaban ƙasar ta Kenya Samuel Ruto wajen jana’izar da zata faru ranar Juma’a 23 ga watan Fabarairu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *