January 15, 2025

Ɗan majalisa a Najeriya zai aurar da marayu mata guda 100

4
images-2023-11-23T090105.996.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Argungu/Augie ta jihar Kebbi a majalisar wakilai ta kasa Sani Yakubu Noma ya bayyana cewa ya kammala shirye-shiryen taimakon marayu mata 100 domin aurar da su.

Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa da ke yankin Argungu a jihar Kebbi, dan majalisar ya ce shirin auren na ɗaya daga cikin gudunmawar da yake bayarwa wajen kyautata rayuwar marayu a mazabarsa.

Ya ce za a ɗaura auren ne a fadar mai martaba Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ranar Asabar.

“An kafa kwamiti don samun nasarar aiwatar da shirin. Wadanda aka zaba domin a daura musu aure sun fito ne daga kananan hukumomin biyu da nake wakilta a Majalisar Dokoki ta kasa.

“Tuni, na sayi gadaje, katifu, kayan aiki masu mahimmanci da sauran kayayyakin aure ga wadanda suka ci gajiyar,” in ji shi.

4 thoughts on “Ɗan majalisa a Najeriya zai aurar da marayu mata guda 100

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *