January 15, 2025

Ɗan Ƙasar Kamaru Zai Samu Naira Biliyan Ashirin da Uku a Damben Boxing na Dare Ɗaya

1
360084178_246030238215019_6670279282250283126_n

Francis Ngannou ne ke riƙe da kambun ajin masu nauyi na faɗan komai da ruwanka na duniya, har zuwa watan Janairun wannan shekarar yayin da ya raba gari da kamfanin shirya gasar faɗa ta UFC, ya koma PFL.

Haifaffen ƙasar Kamaru mai shekaru 37 ya shirya tsaf don jarraba sa’arsa a kan gwarzo mai riƙe da kambun aji mai nauyi na damben Boxing na duniya.

Wadannan manyan gwaraza za su ɓarje gumi a ƙasar Saudiya a watan Oktoba mai zuwa, inda ake sa ran kowane daga cikinsu zai tashi da kimanin dala miliyan talatin, daidai da Naira biliyan ashirin da uku – ko mutum ya ci, ko bai ci ba.

Mista Ngannou wanda ya isa nahiyar Turai bayan keta Sahara da taikun Bahar Maliya, ya kasance da burin shiga gasar ƙwararrun damben Boxing, kafin ya tsinci kansa a wasa faɗan komai da ruwanka.

Haka kuma, ya yi nasarar zama mafi zafin naushi a duniya, sakamakon wani gwaji da aka yi masa a shekarun baya.

1 thought on “Ɗan Ƙasar Kamaru Zai Samu Naira Biliyan Ashirin da Uku a Damben Boxing na Dare Ɗaya

  1. Арматура диаметром 32 мм, изготовленная из стали марки А500С, является одним из самых востребованных видов металлопроката в строительстве. Она применяется при возведении фундаментов, армировании стен и перемычек. https://armatura32.ru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *