February 10, 2025

Ɗalibin Jama’a A Najeriya Ya Hallaka Kansa Saboda Matsin Rayuwa

1
images-2025-02-05T085311.075.jpeg

Daga The Citizen Reports

Wani dalibi mai matakin karatu na biyu (200 Level) a sashen Kafafen Yada Labarai na Jami’ar Ilorin (UNILORIN), Jihar Kwara, ya kashe kansa bayan fama da matsin tattalin arziki mai tsanani.

Lamarin, wanda ya faru a yankin Oke-odo na Tanke, Ilorin, ya jefa al’ummar jami’ar cikin alhini da jimami.

Rahotanni sun bayyana cewa ɗalibin, wanda ba a bayyana sunansa ba, guba ya sha a cikin gidan da yake.

An ce matsalarsa ta kara ta’azzara ne tun bayan dawowarsa makaranta bara, inda halin rayuwa ya kara tsananta bayan rasuwar mahaifinsa shekaru da suka wuce. Mahaifiyarsa, wacce tsohuwar malama ce, ita kadai ke daukar nauyinsa, amma duk da kokarinta, abin ya gagara.

Abokan karatunsa sun ce sun taba hada masa kudi domin biyan kudin makaranta da sauran bukatun yau da kullum, ciki har da abinci. Duk da haka, ba su iya magance matsalarsa gaba daya ba.

Mummunan lamarin ya faru a karshen mako lokacin da abokin zamansa ya tafi makaranta. Da ya dawo, sai ya tarar da gawarsa da kuma wata takarda da ya bari.

A cikin wasikar, dalibin ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da fuskantar matsin tattalin arzikin da yake ciki ba, wanda ya ce shi ne dalilin da ya sa ya yanke shawarar kashe kansa.

Abokin zamansa ya hanzarta sanar da mutane, inda aka fara bincike kan lamarin. Har yanzu mahukunta ba su fitar da wata sanarwa kan batun ba.

1 thought on “Ɗalibin Jama’a A Najeriya Ya Hallaka Kansa Saboda Matsin Rayuwa

  1. Hey I know this is offf topic buut I was wondering iif youu knew of anny widgets I cold aadd to my blog thst automaticaly tweet myy
    neweat twutter updates. I’ve been loioking forr a plug-in lik this forr quite some time and was hoping mayb yoou wkuld hve slme experieence witrh somethin like this.
    Please llet mee knoiw iff yoou run into anything.
    I tuly enjoy reqding your blog and I look forward tto your new updates.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *