February 16, 2025

Ɗalibar jami’a ta rasa ranta a wajen masu garkuwa da ita

0
IMG-20240905-WA0008

Abdullahi I. Adam

Wata ɗalibar Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Abeokuta a Jihar Ogun, Christiana Idowu, wadda aka yi garkuwa da ita a tsakanin Ikorodu da Yaba a Jihar Legas, ta gamu da ajalinta a hannun wanda yai garkuwa da ita, kamar yadda labaru suka nuna.

Shugaban ƙungiyar ɗalibai na jami’ar ta FUNAAB Ibrahim Adeyemi ne ya tabbatar wa da wakilin jaridar The Punch hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Alhamis.

Adeyemi ya ce, “Ƙungiyarmu ta ɗalibai ta a da tabbacin cewa wanda ya sace ta ne ya kashe ta. Za mu bibiyi lamarin nan ba da jimawa ba.”

A wani ɓangare kuma, ‘yan uwan marigayiyar sun shaida wa jaridar PUNCH a ranar 26 ga watan Agusta cewa masu garkuwa da mutane suna neman kuɗi ₦3m a matsayin kuɗin fansa kafin su saki ɗalibar.

Majiyar ta shaida wa Punch ɗin cewa Christiana ta bar gidanta da ke unguwar Itaoluwo a Ikorodu inda ta nufi Jami’ar Legas da ke yankin Yaba a jihar inda ta ke samun horo kan ƙwarewar aiki kafin masu garkuwa da su sace ta.

Majiyar ta kuma bayyana cewa bayan an kasa samunta na wani ɗan lokaci, masu garkuwan sun tuntuɓi iyalanta ta wayar tarho, inda suka buƙaci a biya kuɗin fansa ₦3m kafin a sako ta.

Majiyar ta ƙara da cewa, bayan da ‘yan’uwan nata sukai ta magiya, sai masu garkuwan su ka amince a biya su naira 350,000 a wani asusu, wanda iyalan suka biya, amma waɗanda suka sace ta suka ƙi sakinta duk da biyansu da aka yi.

A halin da ake ciki yanzu, a wani saƙo da aka wallafa a shafin X, mai amfani da @letter_to_jack ya bayyana cewa jami’an leƙen asiri sun samu nasarar gano inda mai garkuwar yake ta hanyar BVN da bayanan asusun da aka yi amfani da shi wajen karɓan kudin fansa daga dangin.

Sanarwar ta ce, “Binciken da jami’an leƙen asiri suke gudanarwa an soma shi ne tun a ranar 26 ga watan Agusta, don gano bayanan lambar asusun masu garkuwan.”

Tun dai ranar 29 ga watan na Agusta ne hukumomi su ka sanar da bankin Wema halin da ake ciki, kuma ana sa ran damƙe waɗanda ake zargin da zaran an kammala bincike.

Kamar yadda bayanai suka nuna inji jami’an “Binciken da aka yi ya nuna cewa ya iya cire kuɗi ₦100,000 daga asusun yin caca kafin jami’ai su samu kamfanin yin caca su kulle asusun.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *