Ɗaliban jami’a a Nasarawa sun shaƙi iskar ƴanci bayan shafe kwanaki a hannun ƴan bindiga
Daga Sabiu Abdullahi
An sako daliban Jami’ar Tarayya ta Lafia (FULAFIA) guda bakwai da aka yi garkuwa da su kwanaki hudu da suka gabata.
An sako daliban ne a yammacin Lahadi bisa kokarin hadin gwiwa na sojoji da sauran jami’an tsaro.
Shugaban Majalisar Wakilan Dalibai Ibrahim Ogbo ya tabbatar da sakin nasu a wata tattaunawa da ƴan jarida.
Daliban, wadanda suka kunshi mata uku da maza hudu, suna asibitin makarantar har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
An yi garkuwa da daliban ne a daren ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da aka dauke daliban daga matsugunin da suke a kauyen Gandu, lamarin da ya sa ‘yan uwansu suka yi ta zanga-zanga nan take, inda masu zanga-zangar suka bukaci a sako ƴan’uwan nasu tare da yin kira da a kara tsaurara matakan tsaro a yankin.