January 15, 2025

Ɗalibai sun mutu a haɗarin kwale-kwale a jihar Kano

0
IMG-20240501-WA0010.jpg


Daga Sodiqat Aisha Umar

Ana ci gaba da zaman alhini a jihar Kano, bayan da kifewar wani kwale-kwale dauke da wasu ɗalibai a madatsar ruwan karamar hukumar Dambatta.

Ana fargabar cewa mutum biyu sun rasa rayukansu a hatsarin.

Lamarin ya ritsa da su ne bayan da suka shiga kwale-kwalen don yin shawagi a cikin ruwan da ke kusa da makarantar.

Ɗalibai uku ne a cikin jirgin ruwan sai kuma direba, amma dalibi daya ya kubuta tare da direban, yayin da biyu kuma suka bata

Masu aikin ceto mutum biyun da suka bata, sun fito da gawar mutum guda.
Sai dai har kawo hada wannan labari, ba a kai ga gano gawar mutum dayan ba.

Madatsar ruwan da lamarin ya auku da ake kira Thomas Dam, na da tazarar kilomita biyar da kwalejin.

Ana yawan samun haɗarin jiragen ruwa a kasar nan, wanda lamarin ake alakanta shu da yawan amfani da matattun jirage da kuma rashin bin tsari wajen amfani da jiragen ruwan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *