December 7, 2025

‘Ɗalibai sama da miliyan 1 za su fara samun bashi’

IMG-20240521-WA0013.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Shugaban asusun bayar da bashin karatu na kasar nan, Mr Akintunde Sawyerr, ya ce kimanin dalibai miliyan 1 da dubu 200 ne a fadin manyan makarantun gaba da sakandare na gwamnatin tarayya za su samu bashin a kashin farko.

Da yake magana a jiya Litinin kafin bude kafar intanet ta neman bashin a ranar Juma’a, ya ce za a fara bude kafar ne ga daliban makarantun tarayya, wadanda makarantunsu suka riga suka kammala sanya bayanan daliban.

A bayanan da ya gabatar, kamar yadda manema labarai suka ruwaito, shugaban ya ce bashin wanda za a ba wa dukkanin daliban manyan makarantun gaba da sakandare na gwamnati, za a bayar da shi ne kashi-kashi inda za a fara da makarantun tarayya kafin a kai ga makarantun gwamnatocin jihohi.

Shugaban ya ce, hanyoyin biyan bashin maras kudin ruwa, suna da sassauci, kuma dalibi zai fara biya ne shekara biyu bayan kammala aikin yi wa kasa hidima (NYSC) idan har ya samu aiki.