December 7, 2025

Ɓatan ‘Yan Mata (Budurwai)

images-261.jpeg

Daga Sulaiman Badamasi (Mahir)

Na zaɓi duk lokacin da na ci karo ana cikiyar wani abu ko mutum na yaɗa shi a shafina. Wannan na daga gudunmawar da zan iya bayarwa don ko Allah zai sa a samu abin ko mutumin da ya ɓata, kuma a ƙara ankarar da mutane su zama masu taka tsantsan da hukumomi game da halin da ake ciki.

Wata tattaunawa da na yi da Dakta, Associate Professor MI Aminu ta saka ni tuntuntuni game da ɓatan ‘yan mata budurwai a cikin gari, a tsakar rana a galibin lokuta. Daga baya kuma sai a ga sun dawo cikin sauƙi, ba tare da biyan kuɗin fansa ko yi wa al’umma, masoya da su ka yi ta cigiya da addu’o’i cikakken bayanin yadda aka samu wacce ta ɓata ba.

Na tambayi kaina, me ya sa irin wannan ɓacewa da bayyana masu kulle kai ba ta faruwa da maza, yara ko manya, sai ‘yan mata kawai? Me ya sa idan aka sace ragowar mutane ake biyan kuɗin fansa kafin a ƙwato su, ko a kashe su, amma ban da ‘yan mata? Me ya sa ba a samun rahoton ‘yan sanda game da kamen masu garkuwar, kamar yadda ake samu a wasu? Me ya sa idan an same su ba a ganin su cikin mawuyacin hali irin yadda waɗanda aka yi garkuwa da su suke kasancewa? Me ya sa, a mafiya yawan lokuta ba sa daɗewa, ba su fiye kwana ba, wasu lokutan ba sa wuce kwana ɗaya?

A wasu lokutan, irin wannan ɓacewa da ‘yan mata suke yi, yana faruwa ne a garuruwan da ba a san su da samuwar garkuwa da mutane ba.

Ashe lokaci bai yi da ya kamata ayi tambayoyi game da dalilin wannan ɓatan dabo mai sarƙaƙiya dake faruwa da ‘yan mata kaɗai ba?

A gaskiya, tsakani da Allah, da farko dai ina fatan duk wacce ta ɓace Allah ya dawo da ita cikin ƙoshin lafiya, kuma Allah ya tsare ‘yan uwanmu da ba su ɓace ba.

Wani al’amari marar daɗi da nake so na bayyana shi ne, lalacewar zamani ta kai yanzu ana samun samari da suke hurewa ‘yan mata kunne don su shirya wannan wasan kwaikwayo. Yadda abin yake shi ne, wasu lokuta yarinya tana amfani da wannan lokacin tashin hankalin ne don ta samu keɓewa da wasu maza a wani keɓantaccen waje.

Misali, akwai iyayen da su ka yi rahoton ɓatan ‘yarsu, amma da ‘Yan Sanda su ka yi tracking, sai aka same ta a wani gidan ɗalibai, a wani gari, tana tare da su. Da iyayen su ka ɗauke ta, ba a jima ba ta sake dawowa.

Wata kuma a hotel aka same ta tare da saurayi. Za ku iya tuna labarin ɓatan wata shahararriya a kafafen sa da zumunta a baya? Ita ma an ce a can wata jaha mai nisa aka same ta tare da wani Babban Alhaji a cikin hotel da jami’an su ka tsananta tracking.

Wannan rubutun ba ya nufin duk ɓatan da mace budurwa ta yi, wani abu ne makamancin haka. Ko kaɗan. Kawai dai ya bayyana wani ɓangare na ɓacewar ne da ba a farga da shi ba.

Allah ya kare mana ƙannenmu mata daga kowace irin ɓacewa.

Da fatan iyaye za su riƙa tsananta bincike a duk lokacin da yarinya ta dawo, kuma idan an gano wani nau’i na wasa a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kan yarinyar da kuma samarin.

Lalle, ina ba wa iyaye ƙwarin gwiwa da su ci gaba da ɓoye sirrin ‘ya’yansu da na ‘ya’yan wasu a duk lokacin da aka fahimci faruwar irin wannan dasisa, domin babu alkhairi cikin bayyana wa, kuma babu alkhairi cikin rashin ɗaukar mataki.

Da fatan iyaye za su rage buri, su riƙa aurar da ‘yan mata ba sai sun kammala karatu mataki kaza da kaza ba, kuma su rage buri kan maza da Allah ya kawo wa nasu. Wani arziƙin a gaba yake.

Sulaiman Badamasi (Mahir) ne ya rubuta wannan maƙala daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

1 thought on “Ɓatan ‘Yan Mata (Budurwai)

Comments are closed.