Ɓata-gari sun lalata turakun wutar lantarkin Gombe, Yola da Jalingo
Daga Sodiqat Aisha Umar
An jefa al’ummomin garuruwan Gombe, Yola da kuma Jalingo cikin duhu bayan da wasu bata-gari suka lalata turakun wutar lantarki guda huɗu a kan hanyar Jos zuwa Gombe mai karfin mega watt 330.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, kamar yadda babbar manajan kamfanin rarraba lantarki ta kasa (TCN), Ndidi Mbah ta bayyana a ranar Talata.
Ta ce hakan ya janyo katsewar wutar lantarkin da tashoshin Gombe, Yola, da kuma Jalingo ke bayarwa.
Ta kara da cewa, TCN na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an mayar da wutar lantarki a yankunan da abin ya shafa.