Ƴan’uwan mutanen da harin bam ya kashe a Kaduna suna neman diyyar naira biliyan 33 a hannun gwamnati
Daga Sabiu Abdullahi
Biyo bayan mummunan harin da sojoji suka kai kan wani taron Maulidi a jihar Kaduna a ranar 3 ga watan Disamba, 2023, iyalan wadanda suka mutu 53 sun shigar da kara a kan gwamnatin tarayya da sojojin Najeriya.
Shari’ar na neman diyyar naira biliyan 33 saboda rasa ‘yan uwansu da suka yi.
Harin da aka kai ta sama, wanda ya faru a kauyen Tudun Biri, karamar hukumar Igabi, ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama, musamman mata da yara, wadanda ke bikin Maulud.
Yayin da gwamnati ta amince da kuskuren kuma ta aika da wakilai zuwa ga al’ummar, iyalan wadanda abin ya shafa sun bukaci a yi musu hukunci da adalci.
Karar, wanda wakilin iyalan wadanda abin ya shafa kuma lauya Mukhtar Usman ya gabatar, ya saka gwamnatin tarayyar Najeriya, babban lauyan tarayya, da kuma babban hafsan soji a matsayin wadanda ake tuhuma.
A cikin wata takardar shaida da aka shigar da karar, wani shaida kan lamarin, Dalhatu Salihu, ya ba da labarin munanan abubuwan da suka faru a ranar 3 ga Disamba.
Ya bayyana yadda mazauna kauyen suka taru don bikin Maulud lokacin da jirgin saman soji ya bayyana kwatsam ya fara jefa bama-bamai a kan taron.
Salihu ya yi ikirarin cewa bayan harin farko, jirgin ya dawo ya sake jefa bama-bamai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane, yayin da ya yi kiyasin cewa an kashe mutane kusan 93 jimilla.