Ƴan’uwan Isra’ilawan da Hamas ta yi garkuwa da su sun yi zanga-zanga a gaban ofishin Netanyahu
Daga Sabiu Abdullahi
Dubun dubatar masu zanga-zanga ne suka sauka a birnin Kudus bayan wani tattaki na kwanaki biyar daga birnin Tel Aviv domin yin matsin lamba ga gwamnatin Isra’ila kan gaggauta sakin fursunonin da Hamas ke tsare da su a Gaza.
Kimanin masu zanga-zangar 20,000, da suka hada da dangi da abokai kusan 240 na waɗanda aka kama, sun hallara a gaban ofishin Firaiminista Benjamin Netanyahu a ranar Asabar, suna zargin gwamnati da yin watsi da rokonsu na mayar da hankali mayar kan ‘yan uwansu.
A yayin da suke tafiya na tsawon sa’o’i a kan babbar hanyar da ta hada garuruwan biyu, masu zanga-zangar sun rike alluna wadanda ke ɗauke da cewa, “Ku dawo da su gida yanzu.”
Manufar ita ce a tilasta wa gwamnati “ta yi duk abin da za ta iya don dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su,” in ji Noam Alon, mai shekaru 25, wanda aka tafi da budurwarsa, Inbar.
An kama mutanen ne a harin da kungiyar Falasdinawa ta kai kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 1,200.